Kari na biyu cikin mako daya, masu fama da cutar Korona a jihar Gombe sun sake gudanar da zanga-zanga kan rashin kyakkyawawan kula da ake basu duk da suna killace. A ranar Talata, Legit Hausa ta kawo muku rahoton yadda wasu mara lafiya a asibitin koyarwan dake Gombe da cibiyar killacewa dake karamar hukumar Yamaltu Deba suka yi zanga-zanga.
Yayinda ma-aikatan kiwon lafiyan jihar suka samu nasarar shawo kan lamarin masu cutar dake asibitin, sun gagara shawo kan wadanda ke Yamaltu Deba.
Sun cakudu da yan kauyen da suka tayasu yin zanga-zangar inda da yawa cikinsu suka ki dawowa cibiyar killacewan. Wani mazaunin jihar da aka sakaye sunansa ya bayyanawa TheCable ranar Jumaa cewa abinda gwamnatin jihar tayi ya sa suka sake fitowa zanga-zanga yau. Yanzu-yanzu: Karo na biyu, masu cutar Korona suna zanga-zanga kan rashin kula
KU KARANTA: Zanga-zangar Da Aka Yi A Kano Kan Cin amana da Batanci ga Annabi Muhammad
Yace “Bayan zanga-zangan ranar Talata, gwamnatin ta ji kunya, saboda haka ta mayar da hankali kan wadanda ke kwance a cibiyar killacewar garin Kwandon, inda ta manta da wadanda ke asibiti suna tunanin cewa jamian asibitin zasu iya kwantar da hankalinsu.” Amma yayinda marasa lafiyan dake asibtin suka samu labarin cewa an inganta abubuwa a dayan wajen, sun fusata saboda sun ji gwamnati ta manta da su ne saboda basu yi zanga-zanga (kamar yadda na can sukayi ba.)”
”Saboda haka suke zanga-zanga a yau, suna tayar da hankulan mutane har sai lokacin da jamian tsaron suka samu nasarar tarwatsa su.” Wata majiya a asibitin ta bayyanawa TheCable cewa wasu marasa lafiyan sun gudu gidajensu. Kawo lokacin wallafa wannan rahoto, an nemi jin ta bakin kwamishanan lafiyan jihar, Ahmed Gana, amma yaki daukan wayarsa. Za ku tuna cewa bisa kididdigan hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC, akwai mutane 109 masu cutar Korona a jihar Gombe.