• Game Damu
  • NX TV
  • Yanar gizo Booking
NAIJAXTREME
  • News
  • Politics
  • Entertainment
    • Biography
  • Hausa News
  • Sport
  • Article
  • NX Radio
  • NX TV
  • StarHunt
  • More
    • Education
    • Business
    • Music
    • Health
    • DJ MIX
    • Gossip
No Result
View All Result
NAIJAXTREME
  • News
  • Politics
  • Entertainment
    • Biography
  • Hausa News
  • Sport
  • Article
  • NX Radio
  • NX TV
  • StarHunt
  • More
    • Education
    • Business
    • Music
    • Health
    • DJ MIX
    • Gossip
No Result
View All Result
NAIJAXTREME
No Result
View All Result
Home LABARAI

YAKIN BIAFRA: Dalilin da ya sa kabilar Igbo ba su daina korafi, kulafuci da kurari ba – Jagoran Ohanaeze

Aisha Mohammed by Aisha Mohammed
June 2, 2020
in LABARAI
0
0
YAKIN BIAFRA: Dalilin da ya sa kabilar Igbo ba su daina korafi, kulafuci da kurari ba – Jagoran Ohanaeze
0
SHARES
77
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsAppPinterest

Jagoran Kungiyar Kare Muradun Kabilar Igbo Zalla, wato Ohanaeze, Nnia Nwodo, ya ce shekaru 50 bayan kammala Yakin Basasa wanda ya ci rayukan milyoyin jama’a, har yau kabilar su ta Igbo ba ta daina korafi, kulafuci da karaji ba, saboda gwamnatocin da suka gabata ba su warware matsala da dalilan da suka haddasa barkewar yakin ba.

 

Related articles

Soyinka ga Buhari: Muna tunkarar mahallakarmu gabadaya

Soyinka ga Buhari: Muna tunkarar mahallakarmu gabadaya

September 15, 2020

Ondo: Bidiyon yadda zaben gwaji ya haifar da hargitsi yayin da APC ta samu nasara

September 15, 2020

Nwodo ya na magana ne a matsayin sa ba bako sa Sashen Igbo na BBC ta gayyata a ranar Asabar domin tattauna batun Yakin Biafra.

A ranar Asabar din ce aka cika shekaru 50 da kammala Yakin Basasa, wato Yakin Biafra.

Nwodo ya ce har yau gwamnati ba ta warware matsalolin da suka haddasa yakin ba. Dalili kenan su kuma kabilar Igbo ake kallon cewa ba za su taba daina kurari, karaji, korafi da kulafuci ba.

Ya tunatar da irin hazikancin kabilar Igbo, inda ya ce a lokacin Yakin Biafra har filin jirgi suka gina, kuma suka kera jirgin yaki.

A ranar 30 Ga Mayu, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin ydda Coronavirus ta hana IPOB bukukuwan tuna cikar Yankin Biafra shekaru 50

Kabilar Igbo musamman ‘yan Kungiyar Taratsin Kafa Biafra (IPOB), sun sha alwashin yin bukukuwan tunawa ko tayar da tsohon mikin da yankin Basasa ya yi musu, wanda a yau Asabar, 30 Ga Mayu ne aka cika shekara 50 daidai da kawo karshen yakin.

 

Sai dai kuma masu goyon bayan Biafra din a wannan shekarar ba su samu yadda su ke so ba, saboda barkewar Coronavirus a duniya ta rage wa ranar tunawar ta su karsashi da armashi.

Dama dai a baya, kowace shekara ‘yan IPOB kan gudanar da zanga-zangar da sau da dama ba a wanyewa lafiya.

KU KARANTA KUMA: An bukaci a kori Isa Ali Pantami daga mukamin shi kan zargin cin zarafin mata da yayi

An sha yin arangama da jami’an tsaro har ana kashe da dama daga cikin su.

A shekarar 2018 jihohin Kudu maso Kudu sun rufe kasuwanni rif a ranar 30 Ga Mayu. Amma a 2019, umarnin a rufe din bai shiga kunnen yawancin ‘yan kasuwar jihohin ba.

A wannan shekarar ta 2020 kuwa, maimakon zanga-zanga ko umarnin zaman-gida, Kungiyar IPOB ta roki kowa ya yi azumin kwanaki uku tare da yin addu’o’i.

Haka Sakataren IPOB, Emma Power ya sanar cewa “kowa ya gudanar da azumin kwanaki uku, kuma ya yi addu’o’i.”

 

Yakin Biafra A Takaice: Dalilai Uku Na Barkewar Yaki

1. Juyin mulkin 15 Ga Janairu, 1966 wanda ‘yan Arewa suka fassara da cewa kabilar Igbo ne suka kashe manyan shugabanni da sojojin Arewa.

2. Juyin mulkin Mayu, 1966, wanda kabilar Igbo suka fassara da cewa ramuwar-gayya ce sojojin Arewa suka yi.

3. Kisan-rubdugun da aka rika yi wa kabilar Igbo bayan juyin mulkin 1966.

Tarihin Yakin Basasar Watanni 30:

1. Janairu, 1966: An kashe su Sardauna da su Tafawa Balewa.

2. Janairu, 1966: An nada Ojukwu Gwamnan Yankin Gabashin Najeriya.

3. Yuli, 1966: Su Murtala sun yi wa Ironsi juyin mulki, suka nada Yakubu Gowon sabon Shugaba.

4. Yuni Zuwa Oktoba, 1966: Hargitsi a Arewa, wanda ya haifar da kisan kabilar Igbo.

5. Mayu, 1967, Ojukwu ya yi ikirarin kafa ‘Jamhuriyar Biafra, tare da shelar ballewa daga Najeriya.

6. Yuli, 1967: Yakin Basasa ya barke.

7. Oktoba, 1967: Sojojin Najeriya sun ci Enugu, hedikwatar Biafra da yaki.

8. Mayu, 1968: Sojojin Najeriya sun ci Fatakwal da yaki.

9. Afrilu, 1969: Sojojin Najeriya sun kwace garin Umuahia.

10. Janairu, 1970: Ojukwu dan tawaye ya tsere gudun hijira.

11. Janairu, 1970: Biafra ta yi saranda.

Tags: Jagoran OhanaezeNaijaxtreme Labarai
ShareTweetSendPin
Next Post
Sojoji sun kashe Boko Haram 75, sun ceto mutum 35 a cikin Yuni – Hedikwatar Tsaro

Sojoji sun kashe Boko Haram 75, sun ceto mutum 35 a cikin Yuni – Hedikwatar Tsaro

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SEARCH OUR ARCHIVES

Editors Pick

📺 NX TV

📺 NAIJAXTREME TV SUBSCRIBE

https://www.youtube.com/watch?time_continue=4&v=IOn0KPXCB6Y
  • Trending
  • Comments
  • Latest
Boko Haram sun yi wa garin Dapchi luguden wuta, sun banka wa gidaje wuta

Boko Haram sun yi wa garin Dapchi luguden wuta, sun banka wa gidaje wuta

May 19, 2020
Sojojin Najeriya sun kama buhun shinkafa cike da alburusai a jahar Zamfara

Sojojin Najeriya sun kama buhun shinkafa cike da alburusai a jahar Zamfara

February 12, 2020
Daruruwan Sun Kauracewa Kauyukan Su Zuwa Barci Akan tituna a Maiduguri Saboda Tsoron Boko Haram

Daruruwan Sun Kauracewa Kauyukan Su Zuwa Barci Akan tituna a Maiduguri Saboda Tsoron Boko Haram

February 18, 2020
Yadda matasa suka yi wa ‘yar 18 gangami suka ci zarafinta a Kaduna

Yadda matasa suka yi wa ‘yar 18 gangami suka ci zarafinta a Kaduna

May 16, 2020
Soyinka ga Buhari: Muna tunkarar mahallakarmu gabadaya

Soyinka ga Buhari: Muna tunkarar mahallakarmu gabadaya

0

An Kama Mutane 6 Don Yin Bayyanar Ma’aikatan Kasuwanci A Katsina

0
LABARAI Yan ta'adda sun kai farmaki hanyar Maiduguri-Damaturu, sun kashe 9

Yan ta’adda sun kai farmaki hanyar Maiduguri-Damaturu, sun kashe 9

0
Rundunar soji ta yanke wa wasu sojoji uku hukuncin daurin shekaru 10

Rundunar soji ta yanke wa wasu sojoji uku hukuncin daurin shekaru 10

0
Soyinka ga Buhari: Muna tunkarar mahallakarmu gabadaya

Soyinka ga Buhari: Muna tunkarar mahallakarmu gabadaya

September 15, 2020

Ondo: Bidiyon yadda zaben gwaji ya haifar da hargitsi yayin da APC ta samu nasara

September 15, 2020
dubi-kyawawan-hotunan-kasaitaccen-biki-na-kannen-uwargidar-gwamnan-jihar-kogi

Dubi kyawawan hotunan kasaitaccen biki na kannen uwargidar gwamnan jihar Kogi

September 13, 2020
Farashin kayan abinci ya fadi warwas a jihar Taraba, a Kano, Katsina, Benue da Nasarawa abun babu sauki

Farashin kayan abinci ya fadi warwas a jihar Taraba, a Kano, Katsina, Benue da Nasarawa abun babu sauki

September 13, 2020

✉ Contact Us

NAIJAXTREME

NaijaXtreme ita ce shafin yanar gizo mafi girma dauke da muhimman labarai, labaran nishadi, wasanni, labaran shahararrun mutane, ado da kwalliya dakuma labaran yau da kullum.

Categories

  • Article
  • Biography
  • Breaking News
  • Business
  • DJ MIX
  • Education
  • Entertainment
  • Gossip
  • HEADLINES
  • Health
  • Movie
  • Music
  • News
  • NX TV
  • Politics
  • Sport

Recent Posts

  • Soyinka ga Buhari: Muna tunkarar mahallakarmu gabadaya September 15, 2020
  • Ondo: Bidiyon yadda zaben gwaji ya haifar da hargitsi yayin da APC ta samu nasara September 15, 2020
  • Dubi kyawawan hotunan kasaitaccen biki na kannen uwargidar gwamnan jihar Kogi September 13, 2020
  • Farashin kayan abinci ya fadi warwas a jihar Taraba, a Kano, Katsina, Benue da Nasarawa abun babu sauki September 13, 2020

Newsletter

Our applications for phones
google play app store
  • Game Damu
  • NX TV
  • Yanar gizo Booking

© 2020 NaijaXtreme.

No Result
View All Result
  • News
  • Politics
  • Entertainment
  • Hausa News
  • Sport
  • Article
  • NX Radio
  • NX TV
  • StarHunt
  • More
    • Education
    • Business
    • Music
    • Health
    • DJ MIX
    • Gossip
    • Biography

© 2020 NaijaXtreme.

Login to your account below

Forgotten Password? Sign Up

Fill the forms bellow to register

All fields are required. Log In

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In