Babbar kotun rundunar sojin Najeriya da ke Abuja ta yankewa wasu sojoji uku hukunci a kan kisan kai – Sojojin da aka gurfanara gaban kotun sun hada da Manjo Akeem oseni, Manjo Ogbemudia Osawe da kuma Laftanal Nuhu Dogary
An yanke musu hukuncin ne sakamakon azabtar da wani Collins Benjamin, soja mai mukamin Lance Corporal, wanda hakan yayi sanadin mutuwarsa shekaru uku da suka gabata A ranar Juma’a, 7 ga watan Fabrairu ne rundunar sojin Najeriya ta yankewa wasu sojoji uku hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10 a kan laifin kisan kai.
Sojojin da aka yankewa hukuncin sun hada da Manjo Akeem Oseni, manjo Ogbemudia Osawe da Laftanal Nuhu Dogari, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito. An kama sojojin ne da laifin azabtar da wani Collins Benjamin, soja mai mukamin lance corporal wanda hakan yayi sanadin mutuwarsa. Rundunar soji ta yanke wa wasu sojoji uku hukuncin daurin shekaru 10
Amma kuma an wanke tare da sakin wani soja mai suna Amosun mai mukamin Kaftin. A wani rahoton na daban, kwamandan Operation Lafiya Dole, Olusegun Adeniyi, ya ce mayakan Boko Haram ba zasu kara kama ko ina na Najeriya. Legit.ng ta ruwaito cewa, Adeniyi ya sanar da hakan ne yayin duba da kokarin da sojin Najeriya ke yi a yankin Arewa maso gabas din a ranar Juma’a, 7 ga watan Fabrairu, a garin Maiduguri da ke jihar Borno.
Ya ce sojin sunyi nasarar nakasa ‘yan ta’addan. Ya ce an fi karfinsu tun 2017 kuma ba zasu kara tasowa ba.